Pakistan ta harbo jirgin saman Indiya a yankin Kashmir

Rundunar Sojin Pakistan ta sanar da harbo wani jirgin yaki mara matuki na Indiya da ya karya ka'idar amfani da sararin samaniyarsu a yankin Kashmir.

1394682

Jirgin ya shiga yankin Pakistan da nisan mita 600.

Sanarwar da Sashen Hulda da Jama'a na Rundunar ta ce jirgin na sanya idanu da bincike mara matuki ya keta ka'idar amfani da sararin samaniyar Pakistan a yankin Sank na Kashmir.

Sanarwar ta ce wannan jirgi ya karya yarjejeniyar amfani da sararin samaniya da ta tsagaita wuta da aka kulla a shekarar 2003 tsakanin kasashen 2 inda ya shiga yankin Pakistan da nisan mita 600.

Sanarwar da Shugabannin Soji suka yi ga kafafan yada labarai na Pakistan ta ce jirgin ya dauki hotunan cibiyoyin sojin Pakistan a yankin, kuma an isharar za a kai wa wuraren hare-hare.

A watan Maris din shekarar da ta gabata Pakistan ta harbo wani jirgin saman Indiya mara matuki inda ta ce an ayi amfani da shi wajen leken asiri.

 Labarai masu alaka