Dakarun Isra'ila sun kama wani Ministan kasar Falasdin

Dakarun Isra'ila sun kama Ministan Harkokin Kudus na kasar Falasdin Fadi Al-Hadmi a yayin wani sumame da suka kai gidansa da asubahin Juma'ar nan.

1390516

Rubutacciyar sanarwar da aka fitar daga ofishin Ministan Harkokin Kudus na gwamnatin Falasdin Al-Hadmi ta ce, 'yan sandan Isra'ila da jami'an leken asirin kasar ne suka mamayi gidan Al-Hadmi dake yankin Al-Sawwani na Gabashin Kudus.

Sanarwar ta ce a yayin sumamen an karya kofofin waje da na gidan Ministan, an tura karnuka sun yi bincike a gidan tare da kwace kudi kimanin dala dubu 2,750.

Sanarwar ta kuma ce a yayin sumamen an yi barna sosai a gidan Minista Al-Hadmi, an kuma tafi da shi don amsa tambayoyi, babu wanda ya san musabbabin kama shi da aka yi.

A shekara 1 da ta gabata karo na 4 kenan da 'yan sandan Isra'ila suka kama Minista Al-Hadmi.Labarai masu alaka