Gwamnatin Yaman da 'yan tawayen Houthi sun amince da kiran MDD na tsagaita wuta

Gwamnatin Yaman da 'yan tawayen Houthi sun amsa kiran Majalisar Dinkin Duniya na a tsagaita domin hana cutar Corona (Covid-19) yaduwa a kasar.

1385502

Rubutacciyar sanarwar da gwamnatin Yaman ta fitar ta ce sun amince tare da karbar kiran da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi na a tsagaita domin hana cutar Corona (Covid-19) yaduwa a kasar.

Shugaban Majalisar Siyasar Houthi Mahdi Al-Mashat ya fitar da sanarwa ta kamfanin dillancin labarai na Houthi SABA cewar "Cikin gamsuwa mun amince da kokarin da Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Yaman Martin Griffiths yake yi na ganin an kawo karshen rikicin Yaman."

Mashat ya ce a shirye suke da su yi duk wani shiri ko amincewa da yarjejeniyar da za ta kawo wa jama'a zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya zuwa yanzu ba a samu bullar cutar Corona a kasar Yaman ba.

A baya ma dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga masu rikici da juna a Libiya da su tsagaita wuta.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewar sun ji dadi kan yadda bangarorin dake fada da juna a Libiya suka amince da tsagaita saboda cutar Corona.Labarai masu alaka