Trump: Lokacin sassautawa Iran bai yi ba

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewar lokacin da za a sassautawa kasar Iran bai yi ba.

Trump: Lokacin sassautawa Iran bai yi ba

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewar lokacin da za a sassautawa kasar Iran bai yi ba.

Trump ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter game da kudirin kakabawa Iran sabbin takunkumai wanda majalisar dattawan Amurka ta yi muhawara tare da jefa kuri'a a kai.

Trump ya ce wannan kudiri na da matukar muhimmanci ga Amurka ta fuskar tsaro.

Ya ce "Muna aiyuka masu kyau game da Iran. Lokacin sassautawa bai yi ba."

Trump ya kuma ce mafi yawan Amurkawa na goyon bayan kashe Janaral Kasim Sulaimani na Iran da suka yi.Labarai masu alaka