An kashe masu zanga-zanga da dama a Iraki

Adadin wadanda aka kashe a lokacin zanga-zanga a Iraki ya kai mutane 10, wadanda aka jikkata kuma sun kai mutane 159..

An kashe masu zanga-zanga da dama a Iraki

Adadin wadanda aka kashe a lokacin zanga-zanga a Iraki ya kai mutane 10, wadanda aka jikkata kuma sun kai mutane 159.

Mamban Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Mai Zaman Kanta ta Iraki Ali Beyatli ya shaida cewar a kwanaki 2 da suka gabata an kashe mutane 10 a lokacinda jami'an tsaro suka yi yunkurin tarwatsa masu zanga-zanga.

Beyatli ya kuma ce an jikkata wasu mutane 159 da suka hada da jami'an tsaro 24.

Tun ranar 1 ga watan Oktoban 2019 Jama'ar Iraki suke zanga-zangar adawa da cin hanci da rashawa, rashin kayan more rayuwa, rashin aiyukan yi da tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gida na kasar.Labarai masu alaka