Trump: Ni na dace a baiwa kyautar Nobel ta zaman lafiya ta 2019

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa shi ya fi dacewa a baiwa kyautar Nobel ta zaman lafiya ta shekarar 2019

Trump: Ni na dace a baiwa kyautar Nobel ta zaman lafiya ta 2019

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa shi ya fi dacewa a baiwa kyautar Nobel ta zaman lafiya ta shekarar 2019.

Trump da yake jawabi a gaban dinbin magoya bayanasa a taron siyasa a birnin Toledo dake jihar Ohio.

A yayinda yake sharhi akan rigimar kasarsa da Iran ya yi tsokaci akan kyautar Nobel ta zaman lafiya ta 2019.

Ya bayyana cewa ya kwace masa hakkin kyautar da zaman lafiya duk da bai bayyna suna ba. Inda ya kara da cewa,

"Ni na ayyanar da yarjejeniyar zaman lafiya. Daga bisani kuma sai na ji, an baiwa shugaban wannan kasar  kyautar Nobel ta zaman lafiya ta 2019 domin ya kubutar da kasarsa"

Kyautar Nobel ta zaman lafiya ta 2019 shugaban kasar Ethiopia Abiy Ahmet mai shekaru 43 mafi karancin shekaru daga cikin shugabanin Afirka aka baiwa saboda rawar da ya taka na samar da zaman lafiya da dakatar da yaki tsakanin kasarsa da makwabciyar kasarsa Eritrea.

 

 Labarai masu alaka