Dakarun Siriya da na Rasha sun kashe fararen hula 6 a Idlib

Jiragen saman Rasha da na gwamnatin Siriya karkashin Bashar Al-Assad sun kai harin a yank,in Idlib da aka hana rikici a cikinsa inda suka kashe akalla fararen hula 6 tare da jikkata wasu 10.

Ofishin sanya idanu na 'yan adawa ya bayyana cewar jiragen saman Rasha da na gwamnatin Assad sun kai hari a gundumar Serakib dake Idlib sai kuma kauyukan Kefrenbil da Bidam da kuma unguwannin Kefer Sejne, Brzabor, Maarrathirme, Tuh, Dar, Kebire, Tel Dem da Tel Katra.

Bayanan da aka samu daga majiyoyin tsaron jama'a na Idlib sun cea harin Kefer Sejne an kashe fararen hula 3 inda gwamnatin Assad kuma ta kashe daya-daya a Serakib, Brzabor, Maarrathırme.

Tag: Siriya , Rasha , Idlib

Labarai masu alaka