Ingila za ta dauki 'ya'yan 'yan ta'addar Daesh Ingilawa da aka kashe a Siriya

Ingila ta amince da daukar 'ya'yan 'yan ta'addar Daesh 'yan kasarta da aka kashe a Siriya.

Ingila za ta dauki 'ya'yan 'yan ta'addar Daesh Ingilawa da aka kashe a Siriya

Ingila ta amince da daukar 'ya'yan 'yan ta'addar Daesh 'yan kasarta da aka kashe a Siriya.

Ministan Harkokin Wajen Ingila Dominic Raab ya shaida cewar "Mun samar da hanyar da za su dawo gida, saboda wannan ne abu na daidai da za a yi."

Raab ya kara da cewar za taimakawa yaran su dawo yin rayuwarsu yadda ya kamata, kuma bai katama marayun su kasance karkashin halin yaki ba.

Sakamakon dalilai na tsaro ya sanya ba a bayyana sunayen yaran ba kuma za su zama Ingilawa na farko da aka dakko daga yankunan da a baya suke hannun 'yan ta'addar daesh zuwa Ingila.

Ana bayyana cewar a sansanonin Siriya akwai Ingilawa mata 25 da yara 'yan kasa da shekaru 5 sama da 60.

Raab ya kuma ce a baya Ingila na fargabar dakko mutanen zuwa gida amma a watan da ya gabata sun dauki matakin dawo da su da kuma dukkan yaran da ba su da iyaye.

A baya ma Jamus, Faransa, Kanada da Denmark ma sun dibi yara kanana daga Siriya zuwa kasashensu.


Tag: Ingila , Tsaro

Labarai masu alaka