'Yan majalisa sun tsige Firaministan Haiti

Bayan wani zaman jefa kuri'a a zauren majalisar dokokin Haiti 'yan majalisar sun tsige Firaministan kasar Jean-Henry Ceant.

'Yan majalisa sun tsige Firaministan Haiti

Bayan wani zaman jefa kuri'a a zauren majalisar dokokin Haiti 'yan majalisar sun tsige Firaministan kasar Jean-Henry Ceant.

A majalisar dake da mambobin 103 'yan majalisa 93 ne suka nuna amincewa kan ya sauka.

Tun daga watan Yulin bara zuwa yau Ceant yake kan kujerar Firaministan Haiti.

Ana sukar Firaminista Ceant da laifin gaza tsinana wani abu da zai kyautata rayuwar jama'ar Haiti.

Tag: Haiti , Guguwa

Labarai masu alaka