Mujallar Forbes ta fitar da jerin sunayen mata 100 mafiya karfin fada a ji a duniya

Mujallar Forbes ta fitar da jerin sunayen mata dari da suka fi karfin fada a ji a duniya a shekarar 2018.

Mujallar Forbes ta fitar da jerin sunayen mata 100 mafiya karfin fada a ji a duniya

Mujallar Forbes ta fitar da jerin sunayen mata dari da suka fi karfin fada a ji a duniya a shekarar 2018.

Firaministan Jamus Angela Merkel ta zo na farko a jerin mata da suka fi kowa karfin fada a ji a duniya, inda Firaministar Birtaniya Theresa May ke biye mata baya. Ta ukunsu ita ce Shugabar Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) Christine Lagarde.

Shugaban Rukunin Kamfanunnukan Sabanci dake Turkiyya Guler Sabanci ta zo na 64 a jerin sunayen.

Ga dai mutane 10 na farko na jerin sunayen mata 100 mafiya karfin fada a ji a duniya,  bayan Merkel, May da lagarde sai Shugabar Kamfanin general Motors Mary Barra, Shugabar Asusun Zuba Jari na Fidelity Abigail Johnson, Wadda ta Kafa Asusun Bill & Melinda Gates kuma mataimakiyar Shugabar Asusun Melinda Gates, Shugabar Shafin Youtube Susan Wojcicki, Shugabar Kamfanin Santander Ana Patricia Botin, Shugabar kamfanin Lockheed Martin Marillyn Hewson da Shugaban IBOM Ginni Rometty.

Sunaye 20 sababbi daga bangaren siyasa, aiyuka da sana'o'i sun shiga jerin mata 100 da suka fi karfin fada a ji a duniya a wannan shekarar.

Tun shekarar 2004 mujallar Forbes  take bayar da jerin sunaye mata 100 inda take zabarsa ta hanyar karfi a siyasance, tattalin arziki da yawan ganinsu a kafafan yada labarai.Labarai masu alaka