Alakar Turkiya da Yukren na ci gaba da habaka

A kan wannan batu mun sake kasancewa da sharhin Dr. Cemil Dogac Ipek malami a sashen nazarin kasa da kasa dake jami’ar Karatekin ta nan Turkiyya.

Alakar Turkiya da Yukren na ci gaba da habaka

A tsakaniin Turkiyya da Yukren akwai alaka mai karfin gaske kan tattalin arziki, yawon bude ido da batun yankin Cremea Tatar. A wannan makon za mu duba alakar Turkiyya da Yukren da irin matsayi da marakin da wannan alaka ta zo tare da irin tasirinta a kan Manufofin Turkiyyaa Kasashen Waje.

Turkiyya ta amince da Yukren a matsayin kasa a lokacinda ta samu ‘yancin kai a ranar 16 ga watan Disamban shekarar 1999. An kulla alakar diplomasiyya a tsakanin kasashen 2 a ranar 3 ga watan Fabrairu. Alakar Turkiyya da Yukren ta girmama da kara karfi a shekarar 2011 a lokacinda aka kafa Hukumar Hadin Kai Kan Tuntubar Juna da Nemo Dabarun Cibaga (YDSK). Alkaluman shekarar 2016 sun nuna cewa, Turkiyya na shigar da kaya zuwa Yukren har na dalar Amurka biliyan 1.25. Tana kuma shigar da kaya na dala biliyan 2.55 daga Yukren wanda jarin kasuwancin dake tsakaninsu ya kai dala biliyan 3.8.

Tun daga tattalin arziki har zuwa tsaro, daga yawon bude ido da raya al’adu har zuwa sauran fannoni daban-daban alakar Turkiyya da Yukren na habaka. Hadin kai da tuntubar juna ya kara habaka a shekarar 2014 a lokacinda Rasha ta mamayi wasu yankunan Yukren. Tun shekarar 2013  da aka fara rikici a Yukren, Turkiyya ta fito ta bayyana muhimmanci da ‘yancin da kasar take da shi gaba daya, inda ta fara nuna muhimmanci da ‘yancin Turkawan Crimea. Turkiyya ta tafiyar da wannan batu a matakin kasa da kasa. Haka zalika bayan da aka dawo da rikici a gaber tekuun Black Sea da lokacinda Turkiyya ta mayar da martani bayan Rasha ta shiga rikicin Siriya, alakar ta dauki wani sabon salo.

An samu rikici tsakanin Rasha da Turkiyya musamman bayan an harbo jirgin saman Rasha a iyakarta da Siriya. Wannan abu ya kuma kara karfafa alakar Ankara da Kiev. Duk da yadda daga baya alakar Turkiya da rasdha ta daidaita, amma dai an ga yadda Turkiyya da Yukren suka sake hade kai tare da aiyuka tare.

A ‘yan shekarun nan, samar da kayan tsaro da Tyurkiyya ke yi ya sake zafafa wannan batu na daukar fasahar kere-kere, kasashen NATO ba su ba wa Turkiyya abinda ta ke bukata ba. Gwmnatin Kiev kuma sakamakon rikici a gabashin Yuklren da yadda Rasha ke daukar matakan soji a kanta, ya sanya ta harzuka wajen karfafa rundunar sojinta. Yukren da ta yi shuhra a bangaren samar da makamai ta kasance tana hada kai da Turkiyya dake daya daga cikin kasashe mafiya karfin soji a duniya. Ta haka ne, a shekarar 2014 Ankara da Kiev suka sabunta yarjejeniyar dabarun soji, samar da na’urar hangen nesa da hango jiragen sama, motoci masu sulke, jiragen yaki na sama, makamai masu linzami  jiragen yaki marasa matuki, injinan jiragen yaki, maganadisai da aiyuka a sararin samaniya da bangarori da dama na ci gaba a fannin tsaro. A lkarkashin haka Turkiyya na samar da kayan yaki na Lira miliyan 20 ga dakarun sojin Yukren, ana yin hadin kai tsakanin kamfanin Ukroboronprom na Yukren da Aselsan na Turkiyya wajen samar da makamai. A karkashin yarjejeniyar da aka cimma, an tanadi Aselsan zai samar da kayan sadarwa na zamani don amfani a harkokin yaki. Haka zalika, a watan Yulin 2018 an gudanar da taron tsaro na Turkiyya-Yukren don habaka aiyukan samar da kayan tsaro a tsakaninsu.

Cigaban da aka samu a bangaren yawon bude ido ya sake habaka dangantakar kasashen biyu. Kasshen biyu a shekarar 2012 sun amince da janyewa juna Visa, a watan Yunin 2017 kuma aka fara shiga kasashen ba tare da fasfo ba. ‘Yan kasar Turkiyya da Yukren za su iya shiga kasashen juna da takardar shaidar zama dan kasa, wannan na nuna irin yadda alakarsu ta girmama. Kaso 70 cikin dari na masu fita kasashen waje daga Yukren Turkiyya suke zuwa. A shekarar 2018 an samu kari da kaso 20 na yawan ‘yan yawon bude ido da suka zo Turkiyya daga Yukren idan aka kwatanta da shekarar 2017 da ta gabata. Adadin maziyartan na bana zuwa yau ya kai mutum miliyan 1.3 inda nan da karshen shekara ake sa ran zai kai miliyan 1.5. wannan adadi na nuna cewar Yukren ce kasa ta 7 dake tura mutanenta zuwa Turkiyya. Turkaea dake ziyartar Yukren kuma na daduwa a kowacce shekara inda a shekarar 2018 adadinsu ya kai kusan mutune dubu dari uku.

A ‘yan shekrun nan, irin yadda Turkiyya ta nuna ta damu da Yukren da aiykan da take gabatarwa, ya sanya jama’ar kasar nuna sha’a ga yaren Turkanci. A karkashin haka, aka bude cibiyar Yunus Emre a Yukren, inda ake gabatar da darussan koyar da Turkanci da taken “Yukren da yawa a Turkiyya, Turkiyya da yawa a Yukren”.

Ankara na bayar da dukkan taimakon da ya kamata ga daya daga cikin al’Umar da suka kara karfafa alakar Turkiyya da Yukren wato jama’ar Turkawan Cremea. Tun bayan fara rikicin Yukren, Turkiyya na ci gaba da ganawa da shugaban Turkawan Cremea kuma dan majalisar dokokin Yukren Mustafa Abdıulcemil Kirimoglu. ‘Yan kasar Yukren dake rayuwa a Turkiyya na taka rawa don karfafa alakars kasarsu da Turkiyya kamar yadda Turkawan Cremea da suke rayuwa a Yukren, da na Ahiska da Gok Oguz suke takawa. A lokacinda aka bude sashen nazarin adabin Yukren a jami’ar Istanbul, an fara koyar da darussan yaren Yukraniyanci a cibiyoyi da dama. A karkashin haka an kama cibiyoyin Yukren 12 a Turkiyya inda a Ankara aka bude ofishin kamfanin dillancin labarai na Yukren.

Alakar Turkiyya da Yukren a shekaru hudun da suka gabata ta habaka sosai a bangarorin cigaban tattalin arziki, siyasa, diplomasiyya da raya al’adu. Wannan abu na da daraja ga kasashen 2. Hadin kan kasashen a yankin tekun Black Sea na kara karfi sosai. Kasashen Turkiyya da Yukren za su amfana sosai a aiyukan hadin kai da suke yi a tekun na Black Sea.Labarai masu alaka