Iran ta ce za ta ci gaba da gwada harba makamai masu linzami

Kakakin Rundunar Sojin Iran Manjo Janar Abulfadhl Shirkaji ya fitar da wata sanarwa game da korofain da Amurka ta kai Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na cewar Iran na ci gaba da gwada makamai masu linzami.

Iran ta ce za ta ci gaba da gwada harba makamai masu linzami

Kakakin Rundunar Sojin Iran Manjo Janar Abulfadhl Shirkaji ya fitar da wata sanarwa game da korofain da Amurka ta kai Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na cewar Iran na ci gaba da gwada makamai masu linzami masu zuwa gajeren zango wanda hakan ya saba wa dokokin ka da kasa.

A sanarwar ta Shirkaji ya ce "Za mu ci gaba da gwada harba makamai masu linzami. Za kuma mu ci gaba da samar da su."

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim mai alaka da gwamnatin Iran ya rawaito Manjo Janar Shirkaji na cewa, sun ji Ministan Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo na soki burutsun wai Iran na samar da makamai masu linzami dake iya zuwa gajeren zango kuma wannan abu ya saba wa sashe na 2231 na dokokin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

A martanin da kakakin Rundunar Sojin ta Iran ya mayarwa da Pompeo ya ce "Za mu ci gaba da gwada harba makamai masu linzami. Za mu ci gaba da samar da su. Ba za mu taba neman izinin wata kasa ba kafin mu yi haka.."

Ya ce, wannan abu da suke yi ba ya karkashin wata yarjejeniya, abu ne da kachokan ya shafi tsaron kasar Iran.

Shirkaji ya kuma yi gargadin cewa, kar wata kawar Amurka dake yankinsu ta yi wani kuskure inda ya ce,

"Idan suka aikata wani kuskure to za su gamu da abinda ba su taba gani ba. Amma muna da tabbashin Amurka da kawayenta ba su aikata wani kuskure a Gabas ta Tsakiya ba. Ajami da 'yan koyo ne za su yi wannan kuskure kuma idan suka yi za su girbi abinda suka shuka."

A ranar Asabar din da ta gabata ne Ministan Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya zargi Iran da harba makamai masu linzami da ka iya janyo yaki a duniya.

Pompeo ya ce "Wadannan makamai na da karfin kai hari kan wata kasa ta Turai ko Gabas ta Tsakiya. Gwada wadannan makamai masu linzami ya sabawa sashe na 2231 na dokokin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. Muna kira ga Iran da ta dakatar da duk wani gwajin makami mai linzami da sarrafa Nukiliya don yaki da take yi wanda haka na barazana ga zaman lafiyar duniya."Labarai masu alaka