Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 05.05.2021

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 05.05.2021.

1634241
Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 05.05.2021

Daily Trust: Jaridar Daily Trust da ake bugawa a Najeriya na cewa Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa rikicin Boko Haram na sake kunno kai a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Daily Nigerian: Jaridar Daily Nigerian da ake bugawa a yanar gizo a Najeriya ta ce Jam’iyyar PDP ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC da su yi bayani kan Naira tiriliyan 10.02 da aka ce an kashe kan tsaro.

Vanguard: Jaridar Vanguard da ake bugawa a Najeriya na cewa ya zuwa yanzu mutane 165,233 cutar corona ta kama a kasar.

 

Al-Jazeera (Gidan Talabijin na Katar): Shugaba Recep Tayyip Erdogan da Sarkin Saudiyya bin Salman bin Abdulaziz sun tattauna ta wayar tarho. An tattauna dangantakar kasashen biyu a taron.

al-Düstur (Jaridar Jordan): An ci gaba da tattauna batun sanya mararraba kan iyakokin ruwa tsakanin Labanan da Isra'ila.

al-Quds al-Arabi: Dan sanda Derek Chauvin a Amurka ya bukaci a sake zaman yin shari’a bayan an same shi da laifin kisan dan asalin Afirka, George Floyd.

 

nex24.news: Fasahar tsaro - Turkiyya ta yi nasarar gwada nata roka na kariya ta sama HISAR-A.

Deutsche Welle: Corona - Gwamnatin Jamus ta zartar da dokar da ta tanadi dawo da hakkoki na asali ga wadanda suka yi allurar riga-kafin cutar corona da wadanda suka tsira daga cutar suka warke.

 

El Mundo (Spaniya): Jam'iyyar Jama'a (PP) ta kai wani matsayi na tarihi na bangaren ra’ayin rikau. Ta lashe zaben yanki a cikin birnin Madrid.

El País (Spain): Pablo Iglesias, shugaban Jam’iyyar Unidas Podemos a Spaniya, ya ba da sanarwar barin siyasa bayan gazawar ‘yan ra’ayin rikau a Madrid

Telesur (Venezuela): Mutane 19 sun mutu a cikin zanga-zangar adawa da sake fasalin haraji a Kolombiya tun daga ranar 28 ga Afrilu.

 

Le Figaro: Covid-19: An yi wa kashi huɗu na mutanen Turai allurar riga-kafi, Amurka ta hanzarta kamfen dinta na riga-kafi.

Le Monde: Masar ta tabbatar da cewa ta sayi jiragen yaki 30 samfurin Rafale daga Faransa.

France 24: Ana nufin yiwa mutane miliyan 3 allurar riga-kafin Covid-19 a wannan makon a Faransa.

 

RIA Novosti: Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya bukaci Rasha da ta cika alkawurranta na kasa da kasa.

Lenta.ru: (Ma'aikatar Tsaro ta Amurka) Pentagon ta zargi Rasha da keta tsarin warware rikicin Siriya.

Jaridar Kommesant: Cibiyar Nazarin Virology da Ilimin Kere-kere ta Rasha "Veсtor" tana gudanar da gwajin asibiti kan allurar riga-kafin "EpiVacCorona" da za a samar mai kashin allurai uku.Labarai masu alaka