Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 08.04.2021

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 08.04.2021.

1617086
Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 08.04.2021

Daily Trust: Jaridar Daily Trust da ake bugawa a Najeriya na cewa jihar Abia ta kaddamar da Shirin Bunkasa na shekaru 30.

Daily Nigerian: Jaridar Daily Nigerian da ake bugawa a yanar gizo a Najeriya ta ce jami’an tsaro masu farin kaya sun kama makiyaya 50 dauke da makamai a jihohin Ekiti, Borno da Cross River.

Vanguard: Jaridar Vanguard da ake bugawa a Najeriya na cewa ya zuwa yanzu mutane 163,498 cutar corona ta kama a kasar.

 

Bild.de: Matashi Bajamushe mai shekaru 18 yana cikin jerin mutane mafi arziki a duniya tare da darajar dala biliyan 3.5

Spiegel.de: Masana kimiyya sun kirkiro wani maɓallin adana bayanai don hana afkuwar annoba.

 

El País, Spaniya: Ma’aikatar Lafiya ta Spaniya da jihohi sun amince da soke yi wa mutanen da ba su kai shekaru 60 allurar riga-kafin AstraZeneca ba.

La Vanguardia, Spaniya: Firaministan Spaniya, Pedro Sánchez na ziyarar Angola da Senegal a matsayin wani bangare na sabon shirin aiyukan Afirka.

Infobae, Ajantina: Sabbin matakan da gwamnatin Argentina ta dauka kan kwayar cutar Corona: Soke tarurrukan jama'a, rufe gidajen abinci da wuraren mashaya da dokar hana fita.

 

Al-Quds Al-Arabi: Amurka ta ware dala miliyan 235 karkashin shawarar ci gaba da taimakawa Falasdinawa.

Al Jazeera: Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka: A shirye muke mu dage takunkuman kan Iran, amma tattaunawar nukiliya (a Vienna) za ta yi wuya.

Al-Dustour (Jordan): Kwayar cutar corona a duniya ta yi sanadiyyar mutuwar mutane miliyan 3.5 kuma annobar ta ta'azzara a Turai da Brazil.

 

Le Soir (Belgium): Belgium ta yanke shawara: Za a yi wa mutanen da suka wuce shekaru 55 allurar riga-kafin Astrazeneca.

France 24 (Faransa): Faransa a hukumance ta fara samar da allurar riga-kafin Pfizer/BioNTech

France 24 (Faransa): Amnesty International ta la'anci ƙasashe masu arziki da mamaye alluran riga-kafin corona.

 

Kommersant: A cikin Rasha, yawan fatarar kuɗi ya karu da kashi 81.5 cikin 100 a farkon kwatan 2021.

Gazeta.ru: Kungiyar Adalci ta Rasha ta gabatar da daftarin doka don rage shekarun yin ritaya ga Karamar Majalisar Dokoki, Duma.

RIA Novosti: Sakataren Kwamitin Tsaron Rasha, Nikolai Patrushev ya zargi Amurka da kera makamai masu guba a wuraren nazarin halittu kusa da kan iyakar Rasha.Labarai masu alaka