Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 30.06.2020

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 30.06.2020.

1446127
Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 30.06.2020

Daily Trust: Jaridar Daily Trust da ake bugawa a Najeriya na cewa dakaru sun kassara mahara 4 dauke da makamai a Rafin Kada da ke karamar hukumar Wukari da Yojaa da ke karamar hukumar Donga a jihar Taraba.

Daily Nigerian: Jaridar Daily Nigerian da ake bugawa a yanar gizo a Najeriya ta ce Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Aliyu Abubakar-Musa a matsayin babban jami’in tsaron sa. 

Vanguard: Jaridar Vanguard da ake bugawa a Najeriya na cewa ya zuwa yanzu mutane 25,133 cutar corona ta kama a Najeriya.

 

Le Parisien: Sakamakon zabe a Ile-de-France (har da yankin Paris): Yawan mata a saman biranen yana ƙaruwa (ma'ana yawan adadin magajin gari mata na ƙaruwa).

Le Figaro: Matasa baƙi sun kafa sansani (ba bisa ƙa'ida ba) a Paris (matasa baƙi kusan 70 waɗanda ba su samu takardun izinin zama ba sun kafa sansani a Paris).

Le Soir (Belgium): Shirin murmure Turai: Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron sun ƙaddamar da shirin murmure tattalin arzikinsu sakamakon koma bayan da cutar corona ta haifar.

 

Bild.de: Ba wanda ke bin ka'idodin corona a Jamus kuma.

Deutsche Welle: Kasar Venezuela ta yanke hukuncin korar jakadar EU a cikin ramuwar gayya ga takunkumin EU. 

ard.de: Shugabar gwamnatin Jamus, Merkel ta karbi bakuncin Shugaba Macron na Faransa a Berlin.

 

Al-Jazeera: Mamba na majalisar Turai, Wakili Charles Guerrence ya nemi Hadaddiyar Daular Larabawa da ta hanzarta aiwatar da dokokin kungiyar kwadago ta kasa da kasa (ILO) game da hakkin aiki.

Al Jazeera: Riyadh (Saudiyya) da Washington (Amurka) suna son tsawaita takunkumi a kan Iran.

Al Quds Al Arabi: Iran ta bayar da sammacin kamo Donald Trump (Shugaban Amurka) ta kuma nemi taimako daga Interpol dangane da kisan Sultan Suleymani (Kwamandan Sojojin juyin-juya hali).

Al Raya (Katar): An fara Taron Brussels yau don tallafawa makomar Siriya.

 

El País (Spaniya): Firaministan Spaniya, Pedro Sanchez ya sake komawa ga abokan huldar sa a kasashen ketare tare da ziyara a yau zuwa Mauritania, wanda ya dauki hutu daga yayin annobar.

La Vanguardia (Spaniya): Tarayyar Turai za ta buɗe iyakokin ta zuwa ƙasashe 15 daga 1 ga Yuli. Amurka, Rasha da Brazil ba su cikin jerin sunayen.

Infobae (Argentina): Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya kori Jakadar Tarayyar Turai a Caracas (babban birnin Venezuelan) daga kasar bayan shawarar takunkumin Tarayyar Turai. (Jakadar: Isabel Brilhante Pedrosa).

 

TASS: Ma'aikatar Harkokin Waje ta Rasha: Amurka ta ba da hanya don sake fara gwajin makamin nukiliya.

RIA Novosti: Ma'aikatar Tsaro ta Tarayya ta Rasha (FSB) ta toshe harin ta'addanci a Vladikavkaz.

TASS: Amurka ta tsaurara takunkumin hana fitarwa zuwa Rasha.

 Labarai masu alaka