Jirage marasa matuka sun haifar da ruwan sama a Dubai

A birnin Dubai dake Hadaddiyar Daular Larabawa tsananin zafi da ya kai daraja 50 ya sanya gwamnatin kasar yin ruwan saman wucin gadi da jirage marasa matuka

1678433
Jirage marasa matuka sun haifar da ruwan sama a Dubai

A birnin Dubai dake Hadaddiyar Daular Larabawa tsananin zafi da ya kai daraja 50 ya sanya gwamnatin kasar yin ruwan saman wucin gadi da jirage marasa matuka.

Birnin wanda ke samun matsakaicin milimita 78 na ruwan sama a kowace shekara kuma wacce ke a kada dake daga cikin kasashe 10 a jerin kasashe masu fama da fari, Cibiyar Kula da Yanayi ta Kasa ta samar da ruwan sama na wucin gadi.

An ayyanar da ruwan sama ta hanyar girgiza gajimare da jirage marasa matuka.

A cikin bidiyon da Cibiyar hasashen yanayi ta fitar, an ga cewa yankin da aka yi amfani da fasahar an samu ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Hanyar, da aka fi sani da 'shuka girgije', yana ba da damar digo na ruwa a cikin gajimare su hadu su samar da ruwan sama sakamakon girgiza gajimaren da jirage marasa matuka ke yi.

Binciken, wanda ke da nufin samar da ruwan sama kamar da bakin kwarya, ana yin sa ne tare da hadin gwiwar kwararru daga Jami’ar Reading dake Birtaniya.Labarai masu alaka