Sudan ta soke dokar da ta hana hulda da Isra'ila

Majalisar kasar Sudan ta soke dokar da ta hana hulda da Isra'ila na shekarar 1958 a shirinta na daidaitawa da Isra'ila

1624789
Sudan ta soke dokar da  ta hana hulda da Isra'ila

Majalisar kasar Sudan ta soke dokar da ta hana hulda da Isra'ila na shekarar 1958 a shirinta na daidaitawa da Isra'ila.

Ministan shari'ar kasar Sudan Nasreddin Abdulbari ya yada a shafinsa ta twitter da cewa,

A taron kolin majalisar dattawa da na ministoci da aka gudanar an yanke hukuncin soke dokar da ta sanya kauracewa Isra'ila.
Dokar ta kauracewa Isra'ila na hana duk wani dan kasar Sudan hulda ta ko wace iri da kanfunan kasar Isra'ila da ma kungiyoyin kasar.

Haka kuma dokar ta na hana shiga ko ratsawa da kayayyakin Isra'ila a kasar ta Sudan wacce keda hukuncin daurin shekaru 10 idan mutum ya saba.

 Labarai masu alaka