Mutane 7 da suka karbi allurar riga-kafin Oxford-AstraZeneca sun mutu

Mutane 7 a Ingila da suka karbi allurar riga-kafin sabon nau'in kwayar cutar Corona (Covid-19) na Oxford-AstraZeneca sun mutu sakamakon dunkulewar jini.

1614225

Daga cikin mutane miliyan 18.1 a kasar da suka karbi allurar ta AstraZeneca, 30 sun samu dunkulewar jini. A cewar sanarwar da Hukumar Kula da Magunguna ta Ingila (MHRA) ta fitar, 7 daga cikin wadannan mutane 30 sun mutu.

A cewar MHRA, a halin yanzu babu wata hujja da ke nuna alaƙa tsakanin dunkulewar jini da allurar riga-kafin Oxford-AstraZeneca.

Ana ci gaba da bincike don gano ko akwai alaƙa tsakanin mace-mace da allurar riga-kafin.

Tsakanin 9 ga Disamba da 21 ga Maris, mutane miliyan 15.8 sun karbi kashin farko na allurar kuma mutane milyan 2.2 sun karbi kashi na biyu na allurar riga-kafin Oxford-AstraZeneca a kasar.

Wasu kasashen Turai sun dakatar da amfani da allurar riga-kafin ko kuma takaita amfani da allurar kan cewa yana haifar da dunkulewar jini.Labarai masu alaka