Jirgin sama ya fado a Afganistan

Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a yayin da ya ke sauka a jihar Helmand din Afganistan.

1613557
Jirgin sama ya fado a Afganistan

Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a yayin da ya ke sauka a jihar Helmand din Afganistan.

Ma'aikatar Tsaro ta sanar da cewa, jirgin saman samfurin Black Hawk ya yi saukar gaggawa bayan matsalar da injinsa ya samu a gundumar Nahri Sirac da ke Helmand.

Sanarwar ta ce, jami'an tsaro 3 sun mutu sakamakon hatsarin.

Kungiyar 'yan tawayen Taliban ta ce ita ta harbo jirgin mai saukar ungulu.Labarai masu alaka