An kashe dan bingida dadi a Amurka

An bindige wani dan bindiga dadi a yayinda yake bude wuta a sansanin sojin saman Amurka na Corpus Christi dake birnin Texas

1421717
An kashe dan bingida dadi a Amurka

An bindige wani dan bindiga dadi a yayinda yake bude wuta a sansanin sojin saman Amurka na Corpus Christi dake birnin Texas.

 Dangane ga bayanan da suka fito daga rundunar sojin ruwan Amurkja, maharin ya kai hari da misalin karfe 06.15 a sansanin sojin saman Corpus Christi.

Sanarwar ta kara da cewa a yayinda aka magance maharin soja daya kuma ya raunana.

Jami'in hukumar bincike ta (FBI) Leah Greeves ya sanar da cewa an kame maharin a mace kuma abokan ta'asarsa sun tsere.

Jami'i Greeves ya bayyana cewa harin ta'addanci ne sai dai yaki bayyna dalilin da ya sanya suke ganin hakan.

 


Tag: #hari , #FBI , #Amurka

Labarai masu alaka