Sauyin Daidaito a Libiya

A libiya inda aka kwashe tsawon lokaci ana tafka rikici, sojojin Gwamnatin Hadin Gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa wacce Turkiyya ke goyawa baya ta fara daukar sabon salo

1404677
Sauyin Daidaito a Libiya

A libiya inda aka kwashe tsawon lokaci ana tafka rikici, sojojin Gwamnatin Hadin Gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa wacce Turkiyya ke goyawa baya ta fara daukar sabon salo. A halin yanzu dai, a karon farko sojojin gwamnatin hadin gwiwar ta fara kalubalantar mayakan Hafter kai tsaye. A yayinda sojojin gwamnatin hadin gwiwar suka karbe ikon garuruwa masu muhinmanci; sun yi nasarar isa yar iyakokin kasar da Tunisiya. A ‘yan kwanakin nan sun gudanar da farmaki mai gwabi inda suka yi nasarar karbe ikon yankunan Terhuna.

 

A wanan makon mun kasance tare da Mal Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar dan Adam watau SETA..

 

Mai yunkurin kifar da gwamnati Janar Haftar, ya kaddamar da kalubalantar hukumar kasar ne da MDD ta kafa a daidai lokacin da ya fara samun gudunmowa daga kasashen Haddadiyar Daular Larabawa, Misira, Saudiyya, Faransa, Isra’ila da ma Rasha a baya bayan nan. A yayinda mayakan Janar Haftar suka yi nasarar kafa gwamnati a yankin gabashin kasar, sun kuma yi nasarar karbe ikon iyakan Misira a yankunan garin Tobruk da kuma karbe ikon yankunan garuruwan Derne da Bingazi tare da gudunmowar kasashen da muka ambata a baya. Haka kuma suna yunkurin karbe ikon yankunan Trablus da Misrata. Hafter dai bai kasance ba, face wakilin wadannan kasahe dake da niyyar mamaye Libiya a maimaikon samar da daidaito a cikin gidan kasar. Ita kuwa gwamnatin sulhun da MDD ke goyawa baya, bata samu cikekken goyon baya ba daga hukumomin kasa da kasa. Bugu da kari, baya ga tsarin Musulunci a halattaciyar gwamnatin, tasirin da kasashen  da basu goyama mata baya ke dashi kamar Haddadiyar Daular Larabawa a hukumonin kasa da kasa da kuma rokon da suke yiwa shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya rashin karfin gwiwar gwamnatin.

Turkiyya kuwa ta fito karara ta bayyana matsayinta na kalubalantar mayakan Hafter da kasashen dake goya musu baya, inda ta bayyana bayar da gudunmowarta ga halattaciyar gwamnatin kasar Libiya da MDD ta kafa. A yayinda take iya kokarinta na kar Libiya ta kasance cikin hali irin na Siriya da Misira, tana kuma kokarin gabatar da hanyar siyasa domin kawo karshen matsalar. Duk da kasancewar mayakan Haftar na ci gaba da kalubalantar Trablus bai hana ta dauki matakan yin yarjejeniya tsakanin mayakan haftar da sojojin kasar ba, lamarin da ake ganin zai iya kawo sauyi a matakan da sojoji ke dauka a kasar. A yayinda aka samar da jami’an horarwa ta hadin gwiwa da Turkiyya ke jagoranta, an kuma ci gaba da kula da yankunan Trablus da Misrata. Haka kuma bayar da gudunmowa da aka yiwa sojojin halattaciyar gwamnatin kasar da makamai na zamani kamar jirgin yaki mara matuki kirar TB2 ya sanya ta iya rage karfin gwiwar mayakan janar Haftar a kasar.

A karshe dai, Turkiyya ta yi sanadiyar hana mayakan Hafter da magoya bayansu karbe ikon Trablus sanadiyar karfafa yankunan da ta yi. Haka kuma ta yi kokarin sanya sojojin kasar dakatar da farmakin da ake kai musu da kuma sake karbe ikon iyakokin kasar da Tunisiya. Ta kuma yi kokarin kare sararin samaniyar yankin Al-Vatiyye da kuma karbe ikon muhinmin garin Terhuna a kudancin Trablus. Wadan nan dai lamurka ne da suka karfafa ikon halattaciyar gwamnatin kasar a kasar baki daya.

Wannan sharhin Mal Can ACUN ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya..

 Labarai masu alaka