Farmakin Garkuwar Bazara da Turkiyya ta kaddamar a Siriya

Abubuwan da suka faru a yankin Idlib a cikin ‘yan makonnin da suka gabata na nuni ga bude wata sabuwar shafi game da rikicin Siriya

1373694
Farmakin Garkuwar Bazara da Turkiyya ta kaddamar a Siriya

A cikin maudu’inmu na yau mun kasance tare da Dkt. Murat Yeşiltaş daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazari akan Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau   SETA ……

Abubuwan da suka faru a yankin Idlib a cikin ‘yan makonnin da suka gabata na nuni ga bude wata sabuwar shafi game da rikicin Siriya. Gwamnatin Asad da Rasha ke goyawa baya ta nuna halin kin kari ga sojojin Turkiyya a yunkurinta na karbe ikon muhimman yankunan da suka hada da titunan M4 da M5 a Idlib. A cikin ‘yan kwanaki kadan Idlib ta kasance abin tattaunawa a bakunan hukumomin kasa da kasa. Hari ta saman da gwamnatin Siriya ta kaiwa sojojin Turkiyya a yankin a ranar 27 ga watan Febrairu lamarin da ya yi sanadiyar shahadar sojojin Tiurkiyya 33 ya kara jagule lamarin yankin a yayinda Turkiyya ta mayarwa gwamnatin Siriyar da martanin da ya dace. Tun da aka fara yaki a Siriya wannan ne karon farko da kasashen biyu suka kalubalanci juna a irin wannan mataki. Matakin da Turkiyya ta dauka ya sanya dukkanin masu ruwa da tsaki a rikicin na Siriya sake dubu matsayinsu da kuma yin waiwaye ga rawar da suke takawa a kasar.

 

Mun kasance tare da Dkt. Murat Yeşiltaş daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazari akan Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau   SETA ……

 

Farmakin Garkuwar Bazarar da Turkiyya ta kaddamar a Siriya ya bayyana irin sauyin da rikicin na Siriya ya samu. Tun bayan fara yakin basasa a kasar Siriya, Turkiyya da Siriyan ba su taba kalubalantar juna kamar yadda suke yi ba a halin yanzu. Duk da rufe sararin samaniyar kasar da aka yi ga jiragen yakin Turkiyya, Turkiyyar ta yi amfani da jiragen yakinta marasa matuka don kai farmakai da ta lalata makamai mallakar sojojin gwamantin Siriya dake yankunan Idlib. A cikin kwana na biyu da fara farmakin an tabbatar da cewa sojojin gwmantin Siriya hadi da dakarun dake goya mata baya fiye da 2500 sun rasa rayukansu. Bayan haka kuma an lalata tankokin yaki kusan 100 da kuma kakkabo jiragen yaki biyu kirar SU 24 da L 36 mallakar gwamnatin Siriyar. Haka kuma gwamnatin Siriyar ta yi hasarar na’urorin kare sararin samniya, gurnati da wasu motocin sojoji da dama. Hakan na nuna cewa farmakan da Turkiyya ta kai ba ga jami’an sojojin bane kawai, har ma ga kayayyakin yakin kasar lamarin dake nuni ga wani irin dabarun yaki na zamani musanman idan aka kalli farmakan da Ankara ta kai da jirage marasa matuka.

A dukkanin salon wannan yakin manufar da ake dashi bayyana take; abin bukata anan dai shi ne, a tilastawa gwamnatin Siriya mutunta yarjejeniyar Sochi. Sai dai dangane da labaran da ake samu duk da irin hasarar da dakarun gwamnatin Siriyar suka yi, basu da niyyar janyewa daga yankunan da aka kaddamar yankin lumana a yarjejeniyar Sochin. Za’a iya gasganta haka ganin yadda ikon yankin Serakip mai muhinmanci; inda kuma titunan M4 da M5 suke ke ci gaba da sauya hannu. Bugu da kari, duk da Rasha ba ta dauki wani mataki akan hasarar da dakarun gwamnatin Siriya suka yi tun a ranar farko ba, daga bisani an fahimci matsayinta akan lamarin. Tura jami’an tsaro da Moscow ta yi a yankunan Serakip bai kasance komai ba face kange Turkiyya daga fadada inda take samar da lumana da kuma kara kare matsayin Moscow a yankin. Hakan dai na karantar da cewa ya kamata Turkiyya ta sake duban lamarin yankin. Sai dai wannan ba matsala bace da zata sanya Rasha da Turkiyya su kalubalanci juna.

A yayinda Turkiyya ta yi tsayin daka na a ci gaba da mutunta yarjejeniyar Sochi da aka kaddamar kwanakin baya, ana ganin Rasha na da wata manufa na daban. An dai fahimci cewa dukkanin kasashen biyu wadanda suka kasance masu fada aji a yankin basu da bukatar rikicin kasar Siriya ya kara dagulewa. Idan dai kasashen biyu suka yi sulhu suka aminta akan yadda za’a warware matsalar yankin na Idlib dukkaninsu biyu zasu amfana, sabanin haka kuwa ba zai haifawa ko wanensu da mai ido ba, lallai ya kamata su bi hanyar yarjejeniya domin samar da mafita a tsakaninsu dama a yankin baki daya. Hakan ina ganin shi ne hanya madaidaiciya…..

 

Sharhin Dkt. Murat Yeşiltaş daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazari akan Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau   SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya ……

                                                                           Labarai masu alaka