Dusar kankara ta yi ajalin mutane da dama a Indiya

Mutane 8 da suka hada da sojoji 3 ne suka rasa rayukansu sakamakon fadowar tuddan dusar kankara a yankin Jammu Kashmir dake Indiya.

Dusar kankara ta yi ajalin mutane da dama a Indiya

Mutane 8 da suka hada da sojoji 3 ne suka rasa rayukansu sakamakon fadowar tuddan dusar kankara a yankin Jammu Kashmir dake Indiya.

Labaran da tasharNDTV ta fitar na cewa awanni 48 da suka gabataan samu zubar kankara sosai inda tuddanta suka fado a yankunan Kupvara, Baramulla da Ganderbal.

Majiyoyin soji sun ce wasu sojoji 3 da kankarar ta fado tare da dannewa a Kupvara sun mutu.

Majiyoyin sun ce an samu nasarar kubutar da wasu sojojin bayan afkuwar ibtila'in, soja 1 ya jikkata inda har yanzu ba a ga wani guda ba.

A gefe guda kuma, mahukunta sun ce a yankin Ganderbal kuma fararen hula 5 ne suka mutu inda aka kubutar da wasu 4 daga karkashin dusar kankarar.

A Baramulla kuma jama'a sun kubutar da wasu 'yan mata 2.Labarai masu alaka