Guguwar Kammuri za ta kunna kai Filifin

An kwashe mutane 43,000 daga yankin da ke gabashin Filifin sakamakon guguwar Kammuri, wadda ake tsammanin zata doshi yankin.

Guguwar Kammuri za ta kunna kai Filifin

An kwashe mutane 43,000 daga yankin da ke gabashin Filifin sakamakon guguwar Kammuri, wadda ake tsammanin zata doshi yankin. 

Hukumar kula da yanayi ta kasar Filifin ta bayyana cewa ana tsamanin a daren yau ko gobe da safe guguwar Kammuri zata kai saurin kilomita 185 a cikin awa daya kuma zata fara bugun tsibirin gabashin kasar.

Mahukunta sun bayyana cewa guguwar Kammuri wacce aka yi hasashen za ta fi shafan cunkoson mutane a tsibirin Luzon, babban birnin Manila kuma ana sa ran lardunan da ke kewaye za su sami ruwan sama mai yawa.

An bayyana cewa, mutane dubu 43 daga gabashin kasar za a kwashe sakamakon Kamamuri kuma an dakatar da aiki a makarantu.

Kammuri, wanda zata kasance guguwa ta 20 a wannan shekarar a Filifin, zata bi hanya daya da guguwar Rammasun, wadda ta kashe mutane sama da 100 a watan Yulin shekarar 2014.

Guguwar Haiyan wacce ta mamaye sassan kasar a cikin 2013 ta kashe mutane sama da 7,300 kuma sama da mutane miliyan 5 suka yi gudun hijira sakamakon guguwar.Labarai masu alaka