Mummunan hatsari a wata mahakar ma'adanai dake Jamus

Mummunan hatsari ya afku a wata mahakar ma'adanai dake jihar Saksonya-Anhalt ta kasar Jamus inda wasu leburori suka makale a karkashin kasa.

Mummunan hatsari a wata mahakar ma'adanai dake Jamus

Mummunan hatsari ya afku a wata mahakar ma'adanai dake jihar Saksonya-Anhalt ta kasar Jamus inda wasu leburori suka makale a karkashin kasa.

Mahukuntan 'yan sanda sun bayyana cewar wasu abubuwa ne suka yi bindiga a mahakar ma'adanan inda wasu mutanen 2 suka samu munanan raunuka.

Ibtila'in ya afku a karkashin kasa da zurfin mita 700 kuma an tabattatar da mutane 35 da suke a karkashin kasa na nan kalau.

Ana kuma ci gaba da aiyukan neman leburorin da ba a gani ba.

Tag: hatsari , Jamus

Labarai masu alaka