"Musulmi bai da gurbi a Indiya"

Wasu gungun fusattun mabiya addinin Hindu 50 dauke da sanduna da kuma maka-makan kafara sun far wa wani muhallin Musulmai, inda suka yi wa mata,yara kanana da kuma matasa dukar kawo wuka.

"Musulmi bai da gurbi a Indiya"

Wasu gungun fusattun mabiya addinin Hindu 50 dauke da sanduna da kuma maka-makan kafara sun far wa wani muhallin Musulmai, inda suka yi wa mata,yara kanana da kuma matasa dukar kawo wuka.

A yayin da 'yan ta'addan ke kai wa Musulman hari sun dinka cewa "Ku je zuwa Indiya,Musulmi bai da gurbi a duniya",inji shugabannin kafafan yada labarai na arewacin kasar Indiya a ranar Asabar din nan da ta gabata.

Jaridar Hindustan Times kuma ta rawaito wani gaggarumin tashin hankali da ke nasaba da wasan Hockey ya barke a kauyen Bhondsi a ranar Alhamis da yamma,inda aka jikkata Musulmai 11,wadanda dukannin 'yan muhalli daya ne.

Tashar NDTV ta sanar da cewa, kusan mutane 25 zuwa 30 ne rufe Musulman da duka,Kuma a ciki har da wani yaro mai shekaru biyu da haihuwa.

Shugabannin Indiya sun sanar da cewa an kai harin a garin Gurugram a yankin Haryana na arewacin kasar,yayin al'uma ke gudanar da shagulgulan bikin Holi.

'Yan sanda sun dau rahoto game da wannan lamarin,inda a yanzu suke ci gaba da bincike a kai.

Subhash Boken,wani kakakin 'yan sandan Gurugram ya sanar wa kafar yada labarai ta Anadolu Agency ta Turkiyya cewa, "A farko mutanen da suka far wa Musulman ba su da yawa.Amma daga bisani sai suka dinka gayyatar jama'a da su taya su lakada wa musu duka".

Kafafan yada labaran Indiya sun sanar da cewa, maharan sun gayyata Musulna zuwa Pakistan.

"Lamarin ya afku a muhallin Muhammad Sajid, dan asalin Uttar Pradesh" inji jaridar Deccan Herald.

A cewar rahoto, wannan lamarin ya kunno kai ne a daidai lokacin da wasu maza biyu da ke kekuna suka kusanto su tare da ce musu "Me kuke yi a nan? Ku je zuwa Pakistan".

Kazalika rohoton ya kara da cewa,wannan harin da aka kai musu,tsararre kana kitsessen ne shiri na wasu jami'iyyun siyasa masu tsauraran ra'ayoyi na kasar Indiya,wadanda su ne suka daure wadannan maharan gindi.


Tag: indiya

Labarai masu alaka