Erdoğan zai gana da Putin a birnin Sochi

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan zai gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a ranar 14 ga watan Fabrairu a birnin Sochi.

1137901
Erdoğan zai gana da Putin a birnin Sochi

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan zai gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a ranar 14 ga watan Fabrairu a birnin Sochi.

Shugaba Erdoğan da ya halarci tattaunawa kai tsaye a gidan talabijin da radiyon kasar ta Turkiyya ya amsa tambayoyi akan lamurkan da suka shafi al'amurran yau da kullun.

A yayinda shugaba Erdoğan ke bayyana cewar babban manufar Turkiyya shine kare kasar Siriya da kuma daukar matakan siyasa domin kawo karshen rikicin kasar ya kara da cewa: "Mu Bamu bangaren dake son Siriya ta rabu, mu tare da Rasaha da ma Iran a tarukan da muka gudanar a Sochi tun daga farko kawo yanzu mun bayyana manufarmu na kare kasar Siriya"

A yayinda Erdoğan ke bayyana cewar tawaga daga Turkiyya ta isa kasar Rasha inda aka tattauna akan muhimman lamurka ya kara da cewa: "Daga cikin muhimman lamurkan da aka tattauna na farko shi ne ganin kungiyoyin dake yankin sun kaurace nan take, hakan zai haifar da da mai ido, abin alfahari dai shi ne komawar Siriyawa kusan dubu 300 kasarsu. Idan aka kauda kungiyoyi a yankin al'ummar yankin zasu koma gidajensu cikin faraha. Hakika sun fara komawa mu kuma zamu dauki matakan tabbatar da hakan"

Shugaba Erdoğan ya kuma kara da cewa: Ina mai matukar fatan ayi nasara. A yayin da yake bayyana cewar tirelolin makamai 23 anka shiga dasu kasar Siriya, ya tabbatar da cewa dukkanin makaman da aka kama mallakar kasar Amurka ne, ya kuma kara da cewa anan an siyarwa kungiyoyin ta'adda da makamai, wannan wani fanni ne na samun kudin wasu, sabili da haka ba abin mamaki bane aga makaman Amurka a hanun fararen hulan a yankin"

A yayinda shugaba Erdoğan ke tunatarwa akan alkawarin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na janye sojojin kasarsa daga yankin, ya bayyana cewar ına mai matukar fatan dai zasu ayyanar da hakan anan cikin kankanen lokaci. Mu ba ma son mu kasance karkashin kalubale da barazana. A sabili da haka a duk lokacin da muka ga wani abun da zai kawo muna barazana zamu dauki matakan da suka dace cikin gaggawa da dukkan karfin mu, inji shugaba Erdoğan.

 Labarai masu alaka