Saudiyya ce ta kashe Kashoggi

Shugaba Erdoğan da takwarorinsa na duniya sun saurari faifan da ke kunshe da dukannin hujjojin da ke nuna cewa shugabannin masarautar Saudia ne suka bada umarnin kashe dan jarida Jamal Kashoggi.

Saudiyya ce ta kashe Kashoggi

A albarkacin bikin cika karni daya da tsagaita wutar yankin duniya na farko,shugaba Erdoğan da takwarorinsa na duniya sun saurari faifan da ke kunshe da dukannin hujjojin da ke nuna cewa shugabannin masarautar Saudia ne suka bada umarnin kashe dan jarida Jamal Kashoggi.

Da yake bayani a gaban manema labarai, shugaban na Turkiyya ya ce: "A sa'ilin da muka tattauna kan batun kisan Kashoggi mun gayyaci shugabar gwamnatin Jamus, Ankela Merkel da takwarana na Faransa,Macron.Ga wanda ke bukatar sananin ra'ayina kan kisan Kashoggi, zai iya karanta lafuzzan da furta a jaridar Washington Post.Wannan wani al'amari ne da aka jima da kitsa shi,kuma babu makawa, umarnin halaka dan jaridan ya fito ne daga shugabannin masarautar Saudia.Ina matukar girmama mai martaba sarkin Salman, don babu wani abinda zan iya tuhume shi da shi,amma ya kamata mu sake zage damtse don gano ainahin wanda ke da alhaki a wannan ta'asar".

Shugaba Erdoğan ya ci gaba da cewa, "Jami'anmu na leken asiri ba su boye komai ba.Kama daga shugabannin Saudia,Amurka, Canada,Jamus kai har ma da na Burtaniya, sun saurari faifan.A gaskiya abin na matukar tayar da hankali.Saboda a lokacin jami'an tsaron Saudia suka saurari faifan,cewa suka yi,"Watakil wannan mutumin kwaya ya sha.Saboda mashayin kwaya ne kawai ke iya aikata hakan".

Shugaba Erdoğan ya ci gaba da cewa: "A lokacin da na saurari faifan, raina ya yi matukar baci.Ga gaskiya a karara,amma ake ci gaba da yin rufa-rufa.A lokacin da Yarima mai jiran gado ya kira ni ta wayar tarho don ya aika mun babban alkalin kasarsa, na zaci cewa zamu cimma gaskiya cikin kiftawar ido.To sai dai alkalin da ya aiko, ba mai neman gaskiya ba ne, mai nuku-nuku ne da yunkurin badda sawu.Dukannin shugabannin duniya wadanda suka saurari faifan, sun yi matukar girgiza,musamman ma Ankela Merkel,Trump da kuma Macron wadanda suka rasa ta cewa".

 Labarai masu alaka