Dalibai dubu 135 suka nemi tallafin karatu a Turkiyya shekarar bana

Ma’aikatan ilimin Turkiyya ta bayyana cewar dalibai daga kasashe daban-daban dubu 135 ne suka nemi tallafin karatu a Turkiyya a shekarar 2018.

Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ga daliban kasashen waje wato Turkey's Presidency for Turks Abroad and Related Communities (YTB) Abdullah Eren ya bayyanawa kanfanin dillancin labaren Anadolu da cewa dalibai dubu 135,000 daga kasashe 150 suka nemi tallafin karatu a Turkiyya a zangon karatun wannan shekarar.

Da yake kwatantawa dana shekarar 2012 ya ce a waccen shekarar dalibai dubu 42 ne kachal suka nemi tallafin karatun.

Ya kara da cewa a halin yanzu akwai dalibai dubu 17 daga kasashe 160 dake karatu a jami’o’I daban-daban a Turkiyya karkashin tallafin karatun kasar.

Ya kara da cewa za’a dada zuwa dubu 19 a wannan shekarar, kafin shekarar 2023 ana fatan kara yawan daliban zuwa dubu 25.

AALabarai masu alaka