" Abin mamaki, Ingila ta san cewa PKK da PYD daya ne,amma ta kasa cewa komai"

Shugaban kwamitin da ke kula da harkokin wajen Ingila,Tom Tugendhat ya bayyana mamakinsa ganin yadda Burtaniya ta tsuke baki,duk da tana da cikakkiyar masaniya game da alakar da ke akwai tsakanin kungiyar ta'adda ta PKK da PYD.

Tugendhak ya ce : 

"Ya kamata gwamnatin Ingila ta fito fili ta nuna matsayinta kan batun kungiyar ta'adda ta PYD da PKK.Kawo yanzu ma'aikatar harkokin waje ta kasa cewa komai.Bayan wani bincike da majalisar Burtaniya ta share watannin 3 tana yi,ta wallafa wani rubutaccen rahoto mai shafuka 33, game kungiyoyin ta'adda ta PKK da PYD.A wannan rahoton akwai cikakkun bayanai game da alakar da ke tsakanin haramtattun kungiyoyin 2.Amma abin mamaki, ma'aikatar harkokin waje ta tsuke baki, ta kuma rufe idanunta.Tuni Turkiyya ta gano cewa akwai muhimmin 'yan uwantaka tsakanin PKK da PYD, Amurka kuma taki amincewa da hakan,inda take ci gaba da mara wa kungiyoyin baya  tare da basu makamai don yakar Daesh.Saboda haka, lokaci ya zo da ya kamata Burtaniya ta bada ra'ayi"

Tag: ingila

Labarai masu alaka