Farmakan Tafkin Zaman Lafiya

Manufar ita ce zaman lafiya,
ta'addanci ake nufa

An sanar da dokar ta baci a wasu yankunan Faransa

Sakamakon guguwar "Eleanor" an sanar da dokar ta baci a yankuna 48 na Faransa.

An sanar da dokar ta baci a wasu yankunan Faransa

Sakamakon guguwar "Eleanor" an sanar da dokar ta baci a yankuna 48 na Faransa.

Sanarwar da Hukumar Kula da Yanayi ta Faransa ta fitar ta ce, sakamakon guguwar an bayar da sanarwar kar ta kwana a yankuna 48 da ke arewacin kasar inda iska ke gudun kilomita 130 a sa'a daya.

An yi hasashen cewa, munin yanayi a yankunan zai ci gaba har nan da karshen mako kuma hakan zai dagula al'amuran yau da kullum.

Sanarwar ta ce, an hana zuwa wuraren shakatawa da makabartu a yankunan tare da gargadar mutane da su kula sosai saboda guguwar na da hadari.

Mutum 1 ne ya rasa ransa inda wasu 65 duka jikkata a ranar Talatar nan sakamakon guguwar "Carmen" da ta kunna kai wani yanki na Faransa.Labarai masu alaka