Shekaru 4 kotu tana shari'ar kisa a Jamus

Yau shekaru 4 kenan ana shari’a a Jamus bayan kungiyar National Socialist Underground ta kashe wasu mutane 10 wandanda 8 daga cikin su Turkawa ne.

Shekaru 4 kotu tana shari'ar kisa a Jamus

Yau shekaru 4 kenan ana shari’a a Jamus bayan kungiyar National Socialist Underground ta kashe wasu mutane 10 wandanda 8 daga cikin su Turkawa ne.

A ranar 6 ga watan Mayun shekarar 2013 kotu ta fara shari’a kan batun inda yau shekaru 4 kenan.

A hirar da ya yi da kanfanin dillancin labarai na Anadolu ne lawya Selim Narin ya a cikin wata uku 3 zuwa 4 za a kawo karshen shari’ar inda ya ce yanzu haka suna dalilan da suke bukata game da kisan.

Narin ya ce baya tunanin wannan shari’ar ta yi tsayi sosai inda ya ce burin su sune a hukumta babban dan kungiyar ta NSU Beate Zschaepe.

A shekarar 2011 ne dai aka gano cewa kungiyar ta’addan NSU ce ta kashe mutane 10 inda ta dau nauyin hare-haren bam sau biyu kuma ta yi sata a bankuna guda 15 cikin shekarar 2000 zuwa 2007.Labarai masu alaka