CIA: 'Yan ta'addar Daesh na iya kai hare-hare a wasu kasashe

Shugaban Hukumar leken Asiri ta Amurka CIA John Brennan ya yi gargadi kan yiwuwar kungiyar ta'adda ta Daesh ta kai hare-hare a wajen kasashen Siriya da Iraki.

Shugaban na CIA ya yi taro tare da mambobin kwamitin tsaro na majalisar dattawan Amurka inda ya ce, an nufi shugabannin kungiyar a hare-hare ta sama da aka kai musu.

Ya ce, duk da haka amma kungiyar na nuna dagiya da tsaurin rai, kuma sakamakon yadda suke rasa karfi a Siriya da Iraki hakan zai sa su fara kai hare-hare a wasu kasashen daban.

Ya kara da cewa, kungiyar ta bawa dukkan mambobinta horo kan dabarun kai hare-haren, kuma akwai 'yan kasashen Turawa da dama da suke yaki tare da Daesh inda wadannan mutanen na iya zama hanyar kai hare-haren a kasashen Turai.

Brennan ya kara da cewa, akwai yiwuwar 'yan ta'addar su shiga cikin 'yan gudun hijira zuwa kasashen Yamma.

Ya ce, ai abin kunya ne yadda suke yakar kungiyar tare da katse hanyoyin samun kudinta amma kuma sai sake yaduwa take yi.Labarai masu alaka