Mayakan Moqtada al-Sadr sun farwa mabiya Sunni

Mayakan kungiyar Moqtada al-Sadr sun farwa kungiyoyin mabiya Sunni dake Iraki,sakamakon umarnin da suka samu daga Shugabansu na dakatar da hare-hare da ake kai wa ofisoshin Shi'a wadanda Iran ke tallafawa.

Majiyoyin shugannin yankunan Basra, Amara, Kut, Nassiriya da kuma Najaf sun tabbatar da cewa mabiyan Moqtada sun farwa ofisoshin hukumar Sunni ta DAWA,Majalisar koli ta addinin Musulunci ta Iraki ISCI  da kuma ofishin kungiyar Sunni ta BADR.

A yanzu haka babu wani rahoton dake nuna mutuwar wani ko kuma samun wata asarar dukiya.

A ranar Juma'ar nan da ta shude Firaministan kasar Iraki Haider al-Abadi wanda wani mamba ne na DAWA  ya ce za su tsaya tsayin daka domin ganin sun kare kansu.

Reuters

 Labarai masu alaka