Jarumin wasan kwai-kwaiyo Michael Douglas da iyalinsa sun ziyarci Turkiyya

Jarumin fina-finai Michael Douglas da matarsa Catherine Zeta-Jones da kuma yaransu sun ziyarci birnin Istanbul dake Turkiyya domin yin hutu

Jarumin wasan kwai-kwaiyo Michael Douglas da iyalinsa sun ziyarci Turkiyya

Jarumin fina-finai Michael Douglas da matarsa Catherine Zeta-Jones da kuma yaransu sun ziyarci birnin Istanbul dake Turkiyya domin yin hutu.

Jarumin da matarsa da kuma ‘ya’yansu da suka hada da Dylan mai shekaru 19 da Carys mai shekaru 16 sun sauka a filin tashi da saukar jiragen saman Istanbul daga na birnin Darrus Salam dake Tanzania.

Jarumin wasannin Douglas da matarsa Zeta-Jones da ‘ya’yansu sun kasance cikin layi domin duba fasufort dinsu.

Bayan sun karbi kayansu mata da mijin sun da da baya daga amsa tambayoyi daga manema labarai.

Sai dai matafiya da dama sun dakata inda suka tattauna tare da daukar hotuna da Douglas da Zeta-Jones.

Daga bisani jarumin Douglas da matarsa  Zeta-Jones da kuma yaransu sun fice daga filin cikin cikin motar alfarma.Labarai masu alaka