Bukin-baje koli na kungiyar mawaka 'Jambinai'

Shahararriyar kungiyar mawakan Koriya ta Kudu "Jambinai" sun sadu da magoya baya a Ankara.

Bukin-baje koli na kungiyar mawaka 'Jambinai'

Shahararriyar kungiyar mawakan Koriya ta Kudu "Jambinai" sun sadu da magoya baya a Ankara.

A tsakanin iyakokin Fasahar Fina-Finan Koriya ta Kudu na shekarar 2019 ta Ma'aikatar Al'adu, Wasanni da yawon shakatawa ta Koriya, kungiyar mawaka ta "Jambinai" ta sadu da masoya kade-kade a Jami'ar Fasaha ta Gabas ta Tsakiya (METU) a babban dakin taro na Kemal Kurdas.

Jakadan Koriya ta Kudu a Ankara Choi Hong-Ghi da dimbin baƙi sun halarci bikin, kuma an ji dadin kiɗan zamani da wasan kwaikwayon gargajiya na Koriya ta Kudu. 

Shugaban kungiyar Jambinai, İlwoo Lee ya gaida magoya bayan su da yaren Turkiyya kuma ya ce ya yi farin cikin zaman sa a Turkiyya.

An gudanar da bikin baje-kolin ne tare da tallafin Ofishin Jakadancin Koriya ta Kudu a Ankara da Cibiyar Al'adu ta Koriya.Labarai masu alaka