Asalin zuwan Kahwa Istanbul

Ko kun san cewa a karni na 16 aka fara kawo kahwa daga Yaman zuwa Istanbul sannan kuma daga baya Turkawa suka samar da hanyar dafa ta inda ake kiran Kofin Turkiyya?

Asalin zuwan Kahwa Istanbul

Ko kun san cewa a karni na 16 aka fara kawo kahwa daga Yaman zuwa Istanbul sannan kuma daga baya Turkawa suka samar da hanyar dafa ta inda ake kiran Kofin Turkiyya?

A wasu ruwayoyin an bayyana cewa, wasu ‘yan kasasr Siriya Hutm da Shams ne suka kawo “Kofi” zuwa Turkiyya a shekarar 1555.

A zamanin mulkin Kanuni Sulaiman, gwamnan yaman Ozdemir Pasha ya ji dadin wannan abin sha wanda hakan ya sanya shi ya kawo zuwa Fadar Sarki dake Istanbul don gabatar masa da ita. Daga baya sai fada ta samar da masu dafa Kahwa a fadar Sarki. Har ta kai ga an samar da wajen kwana ga masu dafa Kahwa din.

A shekarar 1615 ‘yan kasuwar Venedict da kuma a shekarar 1650 ‘yan kasuwar Mercell suka tallatar Kahwar Turkiyya a duniya baki daya. Ta haka ne ya shiga zuwa Turai.Labarai masu alaka