"Musulmai na wahala don sun ki Allah"

Hamshakin mawakin duniyar Islama na kasar Ingila,Yusuf Islam ya gayyaci Musulmai duniya ga baki daya da su dawo kan tafarkin Allah da na Manzonsa,idan ba haka ba zasu ci gaba da wahala da kuma wulakanta har sai an busa kaho.

"Musulmai na wahala don sun ki Allah"

Hamshakin mawakin duniyar Islama na kasar Ingila,Yusuf Islam ya gayyaci Musulmai duniya ga baki daya da su dawo kan tafarkin Allah da na Manzonsa,idan ba haka ba zasu ci gaba da wahala da kuma wulakanta har sai an busa kaho.

Fitaccen mawaki,marubucin kasida kana babban mai da'awa,Yusuf ya furta wadannan kalaman a ranar Alhamis din nan da ta gabata, a albarkacin babban taron Halal 2018 wanda aka shirya a birnin Santambul na Turkiyya.

Yusuf Islam ya ce, "Kamata ya yi kasashen Musulmai sun samar da hanyoyin cigaba da karan kansu.A yau abin bakin ciki ne ganin yadda babu kasa daya tilo a duniyar Islama,wacce ke iya kere jiragen sama, motoci ko kuma talabijin ba.Al'umar Musulmai ta kauce daga ainahin manufarta ta malami da kuma misali ga duniya ga baki daya,kamar yadda Al Kur'ani mai tsarki ya ambata a cikin surar "Iqra".Ba zamu taba yin nasara ba har sai rungumi Allah da na manzansa.

Kazalika ya kara da cewa: "Yawancin tunace-tunace falsafa wadanda ke hannun riga da akidojin Islama ne suka yi wa kasashenmu na Musulmai katutu.Shi yasa muka tanadi makarantun masu dumbin yawa wadanda ke koyar da ababen a zo a gani,amma ga tambaya: Shin ko ina Ubangiji ya ke? Ina Allah ? Lokaci ya zo da ya kamata a ce Musulmai sun dai tinkaho da kukan rashin martabar da kubuce musu,don gina makomarsa kan kyaukyawan tafirki".

Islam ya shiga duniyar mawaka da kafar dama a wajejen shekarar 1960,inda a lokacin ake kiran sa da suna Cat Stevens,inda daga bisani ya Musulunta a shekarar 1978,abinda ya gina makarantu masu dumbin yawa da kuma gidajen tallafa wa marasa galihu.

Taron Halal 2018 wanda aka kwashe kwanaki 4 ana gudanar da shi a karkashin jagorancin shugaban kasar Turkiyya,ya zo karshe a ranar Alhamis din nan.

Sama da kwastomomi 500,masu baja koli 25, kwararru a fannin ilmi daban-daban daga yankin Gabas ta Tsakiya,gabashi da kuma tsakiyar Turai,yankin Balkan da kuma Afrika ne suka halarci wannan gaggarumin taron.Labarai masu alaka