Libiya: Mun samu sabani da Girka saboda kulla yarjejeniya da Turkiyya

Firaministan Libiya Abdulhamid Dibeybe ya bayyana cewa, sun samu sabani da Girka sakamakon sanya hannu da Turkiyya kan "Yarjejeniyar Ikon Amfani da Iyakokin Teku."

1635206

A tattaunawar da Dibeybe ya yi da tashar Aljazeera ta Katar ya yi bayani game da yanayin da kasarsa ta ke ciki.

Da aka tambaye shi game da yarjejeniyar da Libiya ta kulla da Turkiyya kan Ikon Amfani da Iyakokin Teku, sai ya bayar da amsa da cewa,

"Ba mu da ra'ayi iri daya da Girka game da Yarjejeniyar Ikon Amfani da Iyakokin Teku da muka sanya hannu da Turkiyya. Ba za mu fita daga wannan yarjejeniya dake kare manufofin 'yan kasar Libiya ba."

 Labarai masu alaka