An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 17 a Najeriya

A wasu farmakai da sojoji suka kai a Najeriya an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 17.

1451812
An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 17 a Najeriya

A wani farmaki da sojoji suka kai a Najeriya an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 17.

Kakakin Ma'aikatar Tsaron Najeriya John Enenche ya sanar da cerwar sun kai wa 'yan ta'addar Boko Haram farmaki a yankin Damboa da ke jihar Borno a yankin arewa maso-gabashin kasar.

Enenche ya ce sun kashe 'yan ta'adda 17 a farmakin, inda suka rasa sojojinsu 2 tare da jikkatar wasu 4 sakamakon arangamar da aka yi.Labarai masu alaka