Ambaliyar ruwa a Ivory Coast

Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a Abidjan Babban Birnin kasar Ivory Coast.

1443935
Ambaliyar ruwa a Ivory Coast

Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a Abidjan Babban Birnin kasar Ivory Coast.

Sanarwar da aka fitar daga Hukumar Kare Fararen Hula ta Kasa (ONPC) ta bayyana cewar a garin Abidjan mafi girma a kasar an samu ambaliyar ruwa bayan mamakon ruwan sama da aka yi.

Sanarwar ta ce mutane 5 sun mutu yayinda wani 1 ya bata sakamakon ambaliyar ruwan, kuma an samu asarar dukiya.

Sanarwar ta ce an aike da ma'aikatan ceto zuwa yankin.Labarai masu alaka