An kashe 'yan Boko Haram 75 a Najeriya

A wasu farmakai da aka kai wa 'yan ta'addar Boko Haram a arewa maso-gabashin Najeriya an kashe tsageru 75.

1429657
An kashe 'yan Boko Haram 75 a Najeriya

A wasu farmakai da aka kai wa 'yan ta'addar Boko Haram a arewa maso-gabashin Najeriya an kashe tsageru 75.

Kakakin ma'aikatar Tsaro ta Najeriya John Eneche ya bayyana cewar dakarunsu sun kai wa 'yan ta'addar Boko Haram farmakai a yankunan Banki da Firgi na jihar Borno.

Eneche ya ce a farmakan an kashe mataimakan Shugaban Boko Hamar Abubakar Shekau su 3 tare da karin wasu mambobin kungiyar 72.

Eneche ya kara da cewar wasu daga cikin 'yan ta'addar sun gudu, kuma an kwace makamai da kayan fada da dama daga hannunsu.Labarai masu alaka