Covid-19: Turkiyya ta aike da kayan taimako zuwa Afirka ta Kudu

A ci gaba da yaki da Corona da ake yi a duniya, Turkiyya ta aike da kayan tallafi ga kasar Afirka ta Kudu.

1408098
Covid-19: Turkiyya ta aike da kayan taimako zuwa Afirka ta Kudu

A ci gaba da yaki da Corona da ake yi a duniya, Turkiyya ta aike da kayan tallafi ga kasar Afirka ta Kudu.

Sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta fitar ta bayyana cewar a karkashin yaki da Corona (Covid-19) jirgin dakon kaya na soji dauke da kayan tallafi ya tashi daga Kayseri zuwa Afirka ta Kudu.

Sanarwar ta ce Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ne ya bayar da umarnin a kai kayan taimakon a jirgin dakon kaya na soji samfurin A-400M.

A baya ma Turkiyya ta aike da kayan taimako don yaki da annobar Corona Covid-19 a kasashen Amurka, Italiya, Spaniya, Kosovo, Makedoniya, Sabiya, Bosniya, Ingila, Uganda da Montenegro.

 Labarai masu alaka