An kashe sojoji 5 sakamakon harin bam a Mali

Sojoji 5 sun rasa rayukansu sakamakon wani harin ba da aka kai wa jerin gwanon motocinsu a Mali.

An kashe sojoji 5 sakamakon harin bam a Mali

Sojoji 5 sun rasa rayukansu sakamakon wani harin ba da aka kai wa jerin gwanon motocinsu a Mali.

Kakakin gwamnatin Mali Yahya Sangare ya bayyanawa manema labarai cewar an kai harin bam kan jerin gwanon motocin sojojin a lokacinda suke tafiya a yankin Alatona dake tsakiyar kasar.

Sangare ya bayar da bayanin cewar an kai harin da bam da aka samar da hannu, kuma an fara kai farmakai a yankin.

Tun shekarar 2012 ake samun rikici tsakanin 2yan tawaye da jami'an tsaro a tsakiyar kasar ta Mali.Labarai masu alaka