Daya cikin takwas na yara kanana a Najeriya na mutuwa kafin cika shekaru 5

A Najeriya dake yammacin Afirka daya cikin takwas na yara kanana na mutuwa kafin cika shekaru 5 da haihuwa a duniya.

Daya cikin takwas na yara kanana a Najeriya na mutuwa kafin cika shekaru 5

A Najeriya dake yammacin Afirka daya cikin takwas na yara kanana na mutuwa kafin cika shekaru 5 da haihuwa a duniya.

Hukumar Kula da Yawan Jama'a ta Najeriya (NPC) ta fitar da rahoto mai taken "Binciken Lafiyar Al'umar Najeriya" wanda ya bayyana cewar a kasar yaran kanana na mutuwa sakamakon kamuwa da cututtukan kwalara, zazzabin cizon sauro da typhoid.

Rahoton ya ce a kasar daya daga cikin yara 8 na mutuwa kafin cika shekaru 5da haihuwa, kuma kaso 59 na mata har yanzu a gida suke haihuwa. Wannan yanayi na kara yawan samun mutuwar yaran.

Rahoton ya kara da cewar duk da matakan da ake dauka idan aka kwatanda da shekarar 2013 za a ga ba a samu wani ragi ba a yawaitar mutuwar yaran kanana.Labarai masu alaka