Wani gini da ya rushe ya kashe mutane 17 a Najeriya

Mutane 17 ne suka mutu sakamakon rushewar wani gini mai hawa 7 a garin Fatakwal dake kudancin Najeriya.

Wani gini da ya rushe ya kashe mutane 17 a Najeriya

Mutane 17 ne suka mutu sakamakon rushewar wani gini mai hawa 7 a garin Fatakwal dake kudancin Najeriya.

Shugaban Shiyyar Kudu na Hukumar Bayar da Agaji ta Najeriya (NEMA) Ejike Martins-Udeinya ya bayyana cewa, an ciro jikkunan mutane 17 inda aka kuma samu nasarar kubutar da wasu 31 da ransu.

Martins-Udeinya ya ce, ana ci gaba da aikin kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su.

Rahotanni sun ce,'yan sandan Najeriya sun kama wadanda suka yi ginin sakamakon amfani da kayan gini marasa inganci.

AALabarai masu alaka