An yanke hukuncin daurin shekaru 2 zuwa 7 ga 'Yan Boko Haram a Jamhuriyar Nijar

Kotu a Nijar ta yanke hukuncin daurin shekaru 2 zuwa 7 ga 'yan ta'addar Boko Haram da suka gurfana a gabanta.

An yanke hukuncin daurin shekaru 2 zuwa 7 ga 'Yan Boko Haram a Jamhuriyar Nijar

Kotu a Nijar ta yanke hukuncin daurin shekaru 2 zuwa 7 ga 'yan ta'addar Boko Haram da suka gurfana a gabanta.

Jaridun Kasar sun bayar da labarin cewa, an bayar da hukunci 2 a kotun da ke garin Diffa a kudu maso-gabashin Nijar wanda yanki ne da 'yan ta'addar na Boko Haram suka yi tsamari.

Kotun ta yanke hukunci ga mambobin Boko Haram 17 na shekaru 2 zuwa 7 a kurkuku.

An dage shari'ar mutane 4 zuwa ranar 11 ga watan Oktoba.

A makon da ya gabata ne aka fara shari'ar 'yan ta'addar da aka kama.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun ce, a tsakanin 2015/2017 Boko Haram ta kai hare-hare 244 a Jamhuriyar Nijar tare da kashe mutane 582.Labarai masu alaka