“Muna neman tsarin Rasha daga kaidin Amurka”

Shugaban kasar Sudan Omar Al Bashir, wanda ke zargin gwamnatin Trump da ci gaba da shuka fitina a kasashen Musulmai, ya nemi tsarin Rasha daga kaidin Amurka.

854743
“Muna neman tsarin Rasha daga kaidin Amurka”

Shugaban kasar Sudan Omar Al Bashir, wanda ke zargin gwamnatin Trump da ci gaba da shuka tsirran fitina a kasashen Musulmai, ya nemi tsarin Rasha daga kaidin Amurka.

Omar Al Bashir ya mika kokon baransa ga takwaransa  Vladimir Putin, a ranar Alhamis din nan da ta gabata a yayin wata ganawa da suka yi a birnin Sochin kasar Rasha, inda ya ce :

“Idan muka yi la’akari da yadda Amurka ta daura damara a wajen shuka fitina a gabas ta tsakiya, babu ta yadda za’a yi hankalinmu ya kwanta.Muna kyautata zaton,Amurka ce ummal aba-isar dukannin fitintinun da ke ci gaba da kunno kai a duniyar Islama da kuma Sudan, wacce a yanzu haka ta rabu gida 2.Wannan ya haifar da tabarbarewar tsaro a kasarmu.Abinda yasa muke matukar bukatar tallafin Rasha, don mu kare kanmu daga sharrin Amurka”

 Shugaban na Sudan ya cigaba da cewa :

“A shekarar 1997, Amurka ta kakaba mana takunkumi, sabili da ta zarge mu da alakantuwa da ta’addanci.A shekarar 2006 kuma, ta sake tunkarar mu da wasu sabbin takunkumai, sakamakon martanin da sojojin Sudan suka mayar wa masu tada zaune tsaye a yankin Darfur mai fama da tashe-tashen hankula.Amma a watan da ya gabata, gwamnatin ta Amurka ta lashe aman da ta yi a baya,ta hanyar dage mafi yawa daga cikin takunkuman da ta kakaba mana,inda ta ce Sudan ta fara hawa kan turbar gaskiya, wacce ke da alaka da kare hakkin bil adama da kuma yaki da ta’addanci.Shi yasa muke neman tsarin Rasha daga kaidin Amurka.Haka zalika, muna matukar jinjina ma ta game da namijin kokarin da ta yi a wajen kare kasarmu”

 

 Labarai masu alaka