Majalisar Tunisiya ta jefa kuri'ar amincewa da sabuwar gwamnati

Rashin tabbas da aka samu a cikin siyasar kasar Tunisia ya sa an jefa kuri'ar amince da sabuwar gwamnatin da Yusuf Shahid ya kafa.

Majalisar Tunisiya ta jefa kuri'ar amincewa da sabuwar gwamnati

Rashin tabbas da aka samu a cikin siyasar kasar Tunisia ya sa an jefa kuri'ar amince da sabuwar gwamnatin da Yusuf Shahid ya kafa.

'Yan majalisu 194 daga cikin 217 ne suka kuri'ar amincewar.

A yayin da 167 daga cikin 'yan majalisar suka jefa kuri'ar "eh", 22 kuma sun ce "a'a" inda biyar kuma 5 suka janye.

Ta haka ne aka amince da sabuwar jam'iyya da Yusuf Shahid daga jam'iyyar Nida Tunus ya kafa.

Ana sa ran cewa a cikin makon mai zuwa gwamnatin Habib Es-Siyd zata bar aiki domin Shahid ya ci gaba.

Tarihi ya nuna cewa Yusuf Shahid mai shekaru 41 shi ne farkon samari da zai zama firaministan kasar Tunisia.

Shahid yayi bayani a Majalisar kasar inda ya ja hankalin mutane da cewa, sabuwar gwamnatin da ya kafa zata maida hankali a kan cigaban kasar.

Ya kuma kara da cewa basu da burin sayarda dukiyar mutane ko kuma canza kundin tsarin mulkin kasar.

 Labarai masu alaka