Kotu ta janye hukuncin kisa ga Mursi

A ranar Talatar nan ne aka saurari hukuncin karshe game da hukıncin kisa da kotu a Masar ta yankewa hambararren shugaban kasar Muhammad Mursi tare da wasu mutane 121.

Kotu ta janye hukuncin kisa ga Mursi

Da safiyar yau din nan ne aka fara zaman shari'ar a kotun dake harbar kwalejin 'yan sanda birnin Alkahira.

Ana dai tuhumar Mursi da mutanen da laifukan kai hari gidan yari da aikata manyan laifuka.

Bayan an kawo Mursi a cikin keji tare da sautan mutanen ne aka fara zaman shari'ar. 

A yanzu dai kotun ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga Muhammad Mursi.


Tag:

Labarai masu alaka